Sarki Sanusi ya yabi shugaba Buhari kan gyaran tattalin arzikin Najeriya

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, a kan kafa sabon kwamitin da zai ke bashi shawara a kan harkokin da suka shafi tattalin arzikin kasa (EAC).

Da yake magana da manema labarai a fadarsa ranar Laraba 18 ga watan satamba 2019, sarki Sanusi ya ce shugaba Buhari ya yi abinda ya dace ta hanyar nada kwararrun masana tattalin arziki, da suka san ciki da wajen tattalin arzikin Najeriya, a cikin sabon kwamitin, a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar barazana saboda adawar kasuwanci a tsakanin wasu manyan kasashe.

Sarki Sanusi ya bayyana mambobin kwamitin a matsayin masu gogewa a bangaren tattalin arziki, tare da bayyana cewa yana da yakinin cewa zasu farfado da tattalin arzikin Najeriya.

 

Ya kara da cewa saka irin wadannan kwararrun masana a cikin kwamitin, ita ce shawara mafi alheri da gwamnatin Buhari ta yanke.

Shugaba Buhari ya cancanci jinjina da goyon baya bisa daukan matakin farfado da tattalin arzikin Najeriya da ya dade a cikin mawuyacin hali, domin babu wasu kwararrun masana tattalin arziki da zasu taimaka wa gwamnati ta cimma manufarta fiye da mutanen da Buhari ya nada a cikin EAC.

 

Sannan kuma  sarki Sanusi II ya musanta cewa ya soki manufofin gwamnatin Buhari a kan tattalin arziki, tare da zargin kafafen yada labarai da sauya ma’anar kalamansa.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More