
Sarkin Goza ya koma gida bayan shekaru 5 da guduwa
Sarkin Gwoza Alhaji Mohammed Shehu- Timta ya koma gida bayan shekara biyar da guduwa daga garin sakamakon hare-haren yan Boko Haram.
Sarkin ya koma ne dalilin tsaron da aka samu a garin, rahotanni sun nuna yadda dandazon al’ummar da suka taru a Pulka da manyan titunan Gwoza a ranar Litinin inda suka tarbi Sarkin mai daraja ta daya.
Mataimakin gwamnan jahar Usman Kadafur, Sanata Ali Ndume da wadansu membobin yan majalisun jaha, Dagatai da Hakimai suna daga cikin wadanda suka raka Sarki Shehu-Timta, inda wadanda suka tarbe shi suka yi shigar al’ada irin ta yan Gwoza.
Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa, dawowar Sarkin ya nuna yadda mulkin farar hula ya dawo a yankin, tare da jaddada yanda sabuwar gwamnatinsu take darajta Sarakuna.