Saudiyya ta yi bikon kamfanoni duk da batun kisan Khashoggi

Saudiyya ta tattaro manyan masana’antu da shugabannin siyasa a taronta, ciki har da wadanda suka yakice kasar a shekarar da ta wuce saboda kisan dan jarida Jamal Khasoggi.
Taron wanda ake yi a Riyadh ya samu halartar Sakataren Baitul Malin Amurka Steven Mnuchin, wanda ya ki halartar taron a karon baya.
Wadanda kuma suka sauya ra’ayi tun wancan lokacin sun hada da shugabannin Credit Suisse, Blackstone da BlackRock.
Shugaban bankin HSBC John Flint ya janye daga halartar taron a 2018, amma a wannan karon shugaban rikon kwarya Noel Quinn ya halarta.

Wannan ne karo na uku na taron, wanda a hukumance ake kira Future Investment Iniative, kuma ana kallonsa a matsayin taron tattalin arziki mai muhimmanci na masarautar.
Asusun zuba jari na Saudiyya ke shirya taron kuma duk da lakabinsa, ba shi da wata alaka da taron Tattalin Arziki na Duniya na shekara-shekara a Davos.
Taron ya kasance da ce-ce-ku-ce a bara, inda aka rika alla-wadai bayan da wasu ma’aikatan Saudiyyar suka kashe wani shaharraren mai sukar kasar a cikin ofishin jakadancinta a birnin Santanbul.
Masu shigar da kara a Saudiyya na sauraren karar mutane 11 da suka ce suna da hannu a kisan Khashoggi. Suna neman a bai wa mutane biyar a cikinsu hukuncin kisa.
BBC ta rawaito cewa kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce shari’ar ba ta cika ka’ida ba kuma hukumomin Saudiyya sun toshe hanyoyin gano gaskiyar lamarin.
Manyan mutane da za su gabatar da jawabi ranar Laraba, sun hada da Firai Ministan Indiya, Narendra Modi, Shugaban Babban Bankin Duniya David Malpass da sirikin Shugaban Amurka Jared Kushner.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More