Shaguna 7 gobara ta ce a Kwalejin Kimiyya ta Kano

Hukumar kashe gobara ta Jahar Kano ta tabbatar da barkewar gobara wacce ta kone shaguna Bakwai a cikin Kwalejin Kimiyya ta makarantar kimiyya da fasaha ta Jahar Kano, a matan fada, wanda ke karamar hukumar Nassarawa a  Kano.

Kakakin hukumar kashe gobaran, Saidu Mohammed, wanda ya tabbatar da afkuwan lamarin ga manema labarai ya ce, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 03:08 na yamma.

“Mun sami kiran gaggawa daga Abdullahi Ibrahim, da misalin karfe 03:14 na yamman, cewa gobara ta tashi a cikin makarantar.

Hakan yasa  muka yi gaggawan aikewa da motocinmu na kashe gobara zuwa wajen domin kashe gobarar da ta tashi don gudun kar ta shafi sauran shagunan,” in ji shi.

Yakuma kara da cewa  har yanzun suna kan binciken abun da ya haddasa  tashin gobaran.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More