Sheikh Zakzaky Yana dauke Da Guba A Jikinsa – Likitan sa

Jagoran yan kungiyar Shi’a ta Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky yana  bukatar kulawar gaggawa daga likitoci saboda gubar da ke jikinsa.

Sanarwar na dauke ne a cikin takardar da Mikail Yunus ya karanta wa manema labarai a Abuja, inda  ya bayyana cewa tuni alkalin da ke shari’ar Malamin ya ba da umarnin da a bar likitocinsa su duba shi.

Wanda hakan ya sanya likitocin suka zo daga kasashen waje,ya ce bayyana cewa duk da likitocin sun iso sai da aka kai ruwa rana tsakaninsu da ja mi’an tsaro na farin kaya kan in da za a duba Malamin da mai dakinsa Malama Zeenatundin.

Ya ce an sha wuya kafin jami’an tsaron suka amince da duba Malamin da Mai dakinsa a Kaduna,Domin su da sun dakge cewa dole sai an je Abuja.

Jaridar Leadership a yau ta raiwaito cewa takardar ta ci gaba da bayyana cewa binciken da kwararrun likitocin suka yi ya bayyana cewa Malamin na dauke da guba mai matukar illa ga jikinsa, don haka likitocin suka nemi da a fitar da shi kasar waje don samun kulawa  a asibitin da ke da ingantattun kayan aiki.

Mikail ya ci gaba da bayyana cewa ita ma mai dakin Malamin, wato Malama Zeenatuddin Ibrahim na fama da ciwo a kafafunta da kuma harsasai a jikinta wadanda har yanzu ba a ciresu ba.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More