Shekara ta 12 ina jinya kafin a yanke min kafa ta – Moda

Jarimin fina-finan hausa Sani Idris wanda aka fi sani da sani Moda ya bayyana farin cikin sa na samun saukin da yi, duba da cewa ya kai shekaru goma sha biyu (12) yana fama da jinyar.

Sani moda yace a lokacin da ya kara zuwa asibiti dan likitoci su duba lafiyara sa ,  suka ce masa yanke kafar shine zaifi sauki a gareshi, dadi yaji kamar a masa albishir da kujerar hajji domin iran azabar da yake sha Allah kadai yasani.

Inda ya bayyana cewar bayan an yanke kafar tasa ya samu sauki batare da wani rashin jin dadi a gareshi ba, duba da halin da yashiga Allah ne ya jarrabe shi kuma ya karba hannu biyu-biyu.

Moda yayi  godiya ga dukkanin wadanda  da suka kaimasa ziyarar dubashi da wayan da suka taimakamasa da addu’oi, kudaden sa musamman abokanan sana’ar sa ta wasa hausa.

A karshe yace hakan ba zai hana shi ci gaba da sana’ar sa ba domin kashi 90 na jama’a sun san shi ne a sana’ar wasan kwaikwayo , duba da cewa shi ma’aikacin gwamnati ne  domin  kuwa har ya kai matakin albashi na 13.Kuma ya gode wa Allah da ya barshi da rai har ya karbi jarrabawar sa.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More