Shekaru 57 rabon da ci Liverpool 7 sai a jiya

A karon farko a tarihin kungiyoyin biyu, Liverpool da Manchester United aka ci su kwallaye shida a wasa daya kuma a rana guda.

Tottenham ta lallasa Man United da ci 6-1 inda Aston Villa suka lallasa Liverpool da ci 7-2.

Ollie Watkins ya zira kwallaye uku a ragar Liverpool, Jack Grealish shine ya zama tauraron wasan bayan da Aston Villa ta yi nasarar 7-2 akan Liverpool mai rike da kambun Premier ranar Lahadi.

Mai tsaron ragar Liverpool Alisson bai buga wasan ba saboda rauni da yake dashi a kafadarsa kuma hakan ya nuna amfanin sa kwarai.

Mohamed Salah ya zira kwallaye biyu a raga.
Ga yadda kwallayen suka kasance

O. Watkins (4)
O. Watkins (22)
Mohamed Salah (33)
J. McGinn (35)
O. Watkins (39)
R. Barkley (55)
Mohamed Salah (60
J. Grealish (66)
J. Grealish (75)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More