Shin El’Rufai zai rattaba hannu akan dokar Takaita Wa’azi ta Jahar Kaduna?

Lokota kadan da suka wuce kafin tsohon Shugaban Majalisar Dokoki ta Jahar Kaduna, Aminu Abdullahi Shagali ya bayyana kawo karshen wa’adin majalisar ne, Majalisar Dokokin Jahar Kaduna ta amince tare da tabbatar da dokar takaita wa’azi a jihar. Shagali ya ce za a kuma kafa wata hukuma ta hadakar addinai wadda Gwamna zai nada mata shugaba da kuma wakilai biyu wadanda za su wakilci addinin Musulunci da addinin Kirista.

Haka kuma a karkashin wannan doka za a samar da kwamiti na hadakar addinai a dukkan kananan hukumomi 23  na jahar.

Kudirin dokar yana kunshe da cewa duk wanda ya kunna kaset na wani abu da ya shafi addini da kara sosai ko kuma ya bude lasifika da kara a wajen da jama’a suke ban da masallaci da coci daga karfe 11 na dare zuwa karfe 4 na dare ya aikata laifi. Don haka zai iya fuskantar dauri na a kalla shekara 2 ko tarar Naira dubu 200 ko a hada masa duka biyun.

Dokar ta ci gaba da cewa duk wanda ya ci mutuncin wani a bainar jama’a ko ya yi wasu kalamai na batanci ko na karya ga wani addini wadanda za su iya haddasa tashin hankular al’amma,  ku haddasa fitina  zai fuskanci daurin shekara 6 ko tarar Naira dubu 100, ko a hada masa duka biyun.

Wannan kudiri wanda aka gabatar tun a shekara 3 da suka gabata, kwaskwarima ce da aka yi wa wata doka da dama aka yi ta tun a 1984, domin kare rayuka da kuma dukiyar jama’a daga salwanta sakamakon abin da batanci da kuma wa’azi barkatai ke haddasawa ne Gwamnan Soja na wancan lokaci Iya Kwamanda Usman Mu’azu ya yi dokar bisa kudirin dokar soja Mai lamba 7 a cikin watan Agustan 1984 don takaita wa’azi. Kamar yadda bayanin dokar ya ce, dalilin wannan doka shi ne zai  ba da dama ga masu ilimin addinai kadai su gabatar da wa’azi a cikin fadin jahar.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More