Shin ko kun san a rana mai kama ta yau aka haifi Aamir Khan?

A rana mai kama ta yau, 14 ga Maris 1965 aka haifi tauraron jarumin fina-finan Hindu kuma mai ba da umarni Mohammed Aamir Hussain Khan, wanda aka fi sani da Aamir Khan a Bombay da ke Indiya.

Cikin shekaru talatin da ya shafe yana harkar fim, jarumi Aamir Khan ya fito da kansa a cikin manyan jaruman fina-finan Hindu da tauraruwarsu ke haskawa.

Jarumin ya fara fitowa a cikin fim ne a matsayin jarumi yaro a fim din Yaadon Ki Baaraat (1973),sannan kuma ya fara taka rawa a matsayin cikakken jarumin da ke jagorantar fim a cikin fim din Qayamat Se Qayamat Kat (1988). Daga nan, jarumi Aamir Khan ya ci gaba da fitowa a cikin fina-finan da suka yi kasuwa sosai irinsu Dil (1990) da Raja Hindustani (1996) cikin tsukin shekarun 1990s.


Bayan daina jin duriyarsa da aka yi na tsawon shekaru hudu, Khan ya sake dawowa da karfinsa da fina- finan da suka yi shura a cikin tsukin shekarun 2000s, irin su Fanaa, Rang De Basanti, Ghajini da 3 Idiots. A cikin tsukin shekarun 2010s kuwa jarumin ya zo da fina-finan da suka girgiza duniyar fina-finan Hindu da fina-finai irinsu Dhoom 3, PK, da Dangal.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More