Shin ko kun san a rana mai kama yau aka kafa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid?

A rana mai kama ta yau, 6 ga Maris 1902 aka kafa shahararren kulob din nan na duniya wato Real Madrid, shekaru 116 da suka shude. Ana yiwa kungiyar lakani da Los Blancos (ma’ana Farare).

Kalmar “real” dai tana nufin “na sarauta” a yaren Spaniyanci. Sarki Alfanso na Xlll ne ya rada wa kungiyar sunan tare da yajewa kungiyar ta rika amfani da tambarin kan sarki a jikin rigar kungiyar a shekarar 1920.

Kungiyar na buga wasanninta na gida a sitadiya din Santiago Bernabeu mai cin mutun 81,044 da ke birnin Madrid.

A yanzu dai Real Madrid ce kungiyar kwallon kafa da tafi kowacce kungiya arziki a duniya.

Julian palacios ne dai ya fara zama shugaban kungiyar na farko, yanzu kuma Florentino Perez ne ke shugabantar kungiyar. Santiago Solari ne kocin kungiyar.

Raul ne dan wasan da yafi kiwanne dan wasan buga wa kungiyar wasanni. Ya buga wa kungiyar wasanni 741 daga shekarar 1994 zuwa 2010.

Cristiano Ronaldo ne yafi kowanne dan wasa jefa wa kungiyar kwallo a raga, da yawan kwallaye 450.

Gareth Bale ne dan wasa mafi tsada da kungiyar ta taba kawowa a tarihin kungiyar.

Kungiyar ta lashe Gasar Laliga say 33, gasar Zakarun Turai sau 13, gasar Copa del Rey sau 19, Gasar Supacopa de Espana sau 10, Gasar Copa de la Liga 1, Gasar Copa Eva de Duerte 1, Gasar Euefa Cup 2, Gasar Euefa Super Cup 4, Gasar International Cup 3, Gasar FIFA Club World Cup 4.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More