Shin ko kun san a rana mai kamar ta yau aka haifi Obasanjo?

A rana mai kama ta yau, 5 ga Maris 1937 aka haifi tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Matthew Okikiola Aremu Obasanjo a Abeokuta,jahar Ogun. Mahaifiyarsa ta rasu a 1958, sannan mahaifinsa ya rasu a 1959.

A 1948 ya shiga makarantar firamare ta Saint David Ebenezer da ke Ibogun. Ya shiga makarantar sakandare ta Baptist’s Boys High School da ke Abeokuta daga 1952 zuwa 1957.

Ya shiga aiki soja a 1958.

Obasanjo ya zama shugaban Najeriya a karkashin mulkin soja a 1976 biyo bayan wani yunkurin juyin mulkin da aka yi wa Murtala Muhammed (R.T) Wanda ya rasa ransa a lokacin.

A 1979,Obasanjo ya yi murabus daga kan kujerar shugabancin kasa tare da yin ritaya daga aikin soja, sannan ya mika mulki ga zababben shugaban kasa a karkshin mulkin dimokradiyya, wato marigayi Alh Shehu Aliyu Shagari.

Obasanjo ya sake zama shugaban Najeriya a karkashin mulkin dimokraiyya daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Ya yi aure sau hudu a rayuwarsa, inda matansa biyu suka mutu, sannan ya rabu da guda. Yana da ‘ya’ya 27.

A yanzu yana da shekaru 81 a duniya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More