Shin ko kungiyar Ma’aikata zata tafi yajin aikin?

Shugabannin kungiyar kwadago da kuma wakilan gwamnatin  Najeriya za su ci gaba da tattaunawa dan cimma yarjejeniya kan batun kan  biyan N30,000 mafi karancin albashi ga ma’aikata.

Babban kalubalen shi ne yadda kungiyar kwadago ke bukatar a kara kashi 29 cikin 100 ga ma’aikatan da ke karbar albashin da ya haura N30,000 da kuma wadanda suke matakin aikin gwamnati na 11 zuwa 17.

Kungiyar kwadago tare yan kasuwa sun bai wa gwamnatin Najeriya wa’adin sati biyu wajen  fara aiwatar da biyan mafi karancin albashin na dubu 30,000,  ko kuma su tafi  yajin aiki a ranar 16 ga watan Oktoba 2019.

Amma hasashe na nuna cewa  zai yi wuya a shiga yajin aikin duba da cewa ana ci gaba da tattaunawa a tsakanin bangaroran biyu a yau Laraba 15 ga watan Oktoba 2019.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More