Shin kun san mutumin da yai sanadiyyar rura wutar zanga-zangar #EndSARS?

Babu shakka bai san cewa faifan bidiyon da yake dauka a Ughelli ba, jihar Delta zai haifar da fushin da zai hasala dubban yan Nigeria ba.

Yarima Nicholas Makolomi kawai ya ji cewa ya kamata ya sauke nauyin da ke kansa na ya fadakar da hukumomi da ‘yan Najeriya game da ayyukan da’addancin da wasu daga cikin jami’an ‘yan sanda ke yi.

Amma ana dora shi a shafukan sada zumunta, bidiyon ya yadu sosai yayin da ya haifar da sha’awa musamman tsakanin masu fafutuka da ke adawa da Sashin Yaki da ‘Yan Sanda na Musamman (SARS).

Wannan lamari ya haifar da tashin hankali a duk fadin kasar kuma hakan ya haifar da farma wani jami’in SARS, Sajan Ohwovwiogor Fidelis, a yankin Ughelli Central Garage tare da gungun mutanen da ke kokarin cinna masa
wuta, amma hakan bata faru ba saboda shiga tsakanin da wani bawan Allah ya yi.’yan sanda sun kama Makolomi,
amma ba kafin ya ba da labarinsa ba.

A zantawarsa da jaridar Vanguard da ke fita duk ranar Lahadi, ya ce: “Bayan an kama yaron (JoshuaAmbrose) a ranar Asabar , an ajiyeshi a gefen motar fasinja a bayan kujerar gaba.

“A lokacin da muke tuki a cikin motar mu a bayan motar ‘yan sandan, kwatsam sai yaron ya yi tsalle daga motar ya fadi a kan hanya bayan haka mun bi motar’ yan sanda a yayin da muke daukar bidiyon.

Bidiyon ya sami karbuwa sosai kafin daga bisani ya haifar da fara zanga-zangar #EndSARS tun ranar Laraba da ta gabata.

Zaga-zangar kin jinin ‘yan
sanda wadda babu makawa ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane a Legas da Ogbomoso a jihar Oyo.

Da yake magana da jaridar Sunday Vanguard kan lamarin, Makolomi, wanda ya sake samun ‘yanci a ranar Juma’a daga hannun ‘yan sanda, wanda suka yi barazanar gurfanar da shi kan zargin tayar da rikici da kuma yada labaran karya sabanin dokar yanar gizo, ya ce duk da cewa ya yi kuskure da ya yada bidiyon a shafukan sada zumunta, bai yi nadamar abinda ya aikata ba.

Makolomi,wanda ya kammala karatunsa a makarantar Cibiyar Gudanarwa da Fasaha, IMT, Enugu kuma mahaifin ‘ya’ya biyu ya ce ya dauki hoton bidiyon ne
kuma ya loda a kafafen sada zumunta da zimmar fadakar da’ yan Najeriya, hukumomin ‘yan sanda da gwamnati kan mummunan halin wasu’ yan sanda.

Da yake bayar da cikakkun bayanai game da yadda aka kama shi, Makolomi, dan gidan sarautar Ughelli , ya ce:

“Ina gida a Ughelli lokacin da wani
abokina ya kira ni cewa in hadu da shi a shahararriyar kasuwar nan ta Mall da ke Effurun.
“Amma da zaran na isa kasuwa, a bakin kofa, sai wasu‘ yan sanda suka tare ni suka dauke ni zuwa ofishin ‘yan sanda na Ebrumede.”

Da yake bayyana kansa a matsayin mai nishadantarwa da kuma injiniyan sauti, ya karyata rahotanni cewa ya yada bidiyon ne don ya batawa ‘yan sanda rai.

“Lokacin da na dauki hoton bidiyon, hakika ba wani mummunan nufi a zuciyata. Gaskiya na yi hakan ne a matsayina na dan kasa mai nuna damuwa a kan abin da wasu ‘yan sanda suka yi duk da cewa daga baya na fito ga jama’a ta shafina na sada zumunta na ce wanda abin ya shafa
(Joshua Ambrose) yana raye bai mutu ba kamar yadda aka bayyana a baya” Makolomi ya ce .

“Daga ofishin‘ yan sanda na Ebrumede, an dauke ni zuwa Hedikwatar ‘Safe Delta’ da ke Isele-Azagba inda aka rike ni tsawon kwana uku kafin a kai ni Hedikwatar ’Yan sanda ta Jihar daga inda aka kai ni kotu.

“Yayin da nake tsare, ‘yan sanda ba su taba bugu na ko cin zarafina ba.”

Da aka tambaye shi ko ya yi nadamar
abin da ya aikata, Makolomi, wanda ya bayyana kansa a matsayin wanda yai sanadiyyar haifar da zanga-zangar #ENDSARS, ya ce:

“A zahiri na ji na yi kuskure da bidiyon da ya yadu a yanar gizo, amma ban taba sanin cewa matasan Najeriya sun rigaya sun fusata ba da ayyukan da wasu jami’an ‘yan sanda ba kamar yadda aka nuna a cikin martanin da ya biyo bayan bidiyon.

“Duk da wahalar da na sha da kuma
fitowata daga baya, ban yi nadamar abinda na aikata ba saboda Najeriya dole ta sake zama mai girma kuma abin da na yi shi ne abin da kowane dan kasa zai yi.
“Shawarata ga matasan Najeriya musamman wadanda ke shiga cikin zanga-zangar ta #ENDSARS ita ce, kada su bari a tsokane su sannan a matsa musu su dauki doka a hannunsu muddin suna fafutikar neman biyan bukata.”

Da yake yaba wa karamin Ministan kwadago da samar da aiyuka, Festus Keyamo, da shugaban karamar hukumar
Ughelli ta Arewa, Cif Godwin Adode, game da taimakawa wajen sakin nasa, ya ce:

“Ga gwamnatin Najeriya, ina so in
yaba musu saboda yadda suka tashi tsaye wajen kalubalantar abin cikin hanzari na amsa buƙatun na matasa kasancewar an sanar da su game da
munanan ayyukan wasu ‘yan sanda a cikin ƙasar kuma ina kuma gode wa Cif Keyamo da Adode saboda tsayawa da sukayi wajen saki na.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More