Shin martanin Atiku kan Elisha na da mahimmaci?

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar a babban zaben 2019, ya ce yaga bigiyon dake yawo wanda ake zargin sanata Elisha Abbo da cin zarafin wata mata, inda yace yayi wa sanatan farin sani amma ya kamata matasan shugabanni irinsa su zama abin koyi.

Tuni dai wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP, wadda Sanata Elisha Abbo ya lashe zabe a karkashinta suka fara tofa albarkacin bakinsu a kan lamarin marin wata mata yayi.

Atiku ya wallafa a shafinsa na Twitter  yana cewa, ya kamata jam’iyyar PDP ta dauki matakin ladaftarwa a kan sanatan, sannan ya  shawarce  Elisha da ya fito fili ya nemi afuwa sannan ya mika kansa ga ‘yan sanda domin nuna dattako.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More