Shin ofishin Opay na iya cigaba da aiki a Kano?

Yan sandan Najeriya reshen jahar Kano sun rufe ofishin da yan adaidaita sahu ke biyan kudi ta kafar Intanet mai suna OPay.

An rufe ofishin ne yayin wata sumame da yan sanda suka yi a Kano kan rashin bin dokokin gwamnati da kamfanin baya yi.

The Nation ta ruwaito cewa jami’an tsaro dauke da bindigu sun isa ofishin kamfanin da ke Lodge road a Kano misalin karfe 11 na safe a ranar Alhamis.

Yan sanda sun umurci dukkan ma’aikatan kamfanin da masu adaidaita sahu da ke wurin su fice inda su kayi barazanar kama dukkan wanda bai yi biyaya ga umurnin ba.

Wani wanda abin ya faru a idonsa ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa masu adaidaita sahun suna shirin biyan kudin cinikin su da daren Laraba ne yan sandan suka iso suka tarwatsa su.

Mai magana da yawun yan sandan  jahar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce gwamnatin jahar Kano ce ta bawa rundunar umurnin rufe wurin, inda yace kamfanin na Opay ya saba wasu dokoki da gwamnatin jahar ta kafa masa muddin yana son yin aiki a jihar to kamata yayi su bi ka’idojin da gwamnatin jahar ta kafa.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More