Shin yan Najeriya da aka kwaso daga Afrika ta kuda na iya komawa dan kaddarar su ko lyalansu?

 Wasu Yan Najeriya da aka dawo da su zuwa gida Najeriya daga kasar Afirka ta Kudu sakamakon rikicin kin jinin baki da ya barke wanda yan kasar ke nuna wa yan kasashen waje, sun bayyana cewar, sun dawo Najeriya ba tare da wani abu a hannun su ba ko watan kaddara ba.

Wani dan asalin jahar Ondo mai suna Segun Salau mai shekaru 32 wanda ya kasha shekaru 5 a  kasar ta Afirka ta Kudu. Ya bayyanawa Aminiya cewa, zamansa a Afirka ta Kudu ya kasance ako da yaushe yana cikin fargaba saboda harin da ake kaiwa baki a kasar, a wannan harin da aka kaiwa ‘yan Najeriya an shiga shagon ‘yar uwata inda aka lalata mata kayan shagon tare da yi mata asarar dukiyarta.

Segun ya kara da cewa bashi da wani dalili ko wani abu da zai sashi komawa Afirka ta Kudu a nan gaba saboda sau uku Kenan yana  ganin abin da ake yi wa baki a kasar wanda hakan bai dace ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More