Shirin fim din Kawaye bai wahalar da ni ba – Aisha Humaira 

Jaruma fina-finan hausa Aisha Humaira ta bayyana farin ciki ta na kamala shirin fim din Kawaye lafiya tare da bayyana cewa bubu wani kalubali data fuskanta wajen gudanar da shirin fim din, kasanewar shine shirin fim dinta na farko a Duniya.

@ayshatulhumairah ta bayyana wa OakTV tace dama can ta saba ganin yadda ake shirya fina-fina hausa shi ya sa gudanar da shirin ba zame mata wani sabon abu ba kuma bai zamo mata abun wahala.

Inda ta kara da cewa kasancewar shirin fim din wasan kwaikwayone, domin ba gaske bane wannan dalilin ya bata damar zage dantse wajen ganin ta taka rawar gani yadda ya kamata ta a shirin fim, inda ta bayyanan jin dadin aikin da abokan aikin bisa hadin kai data samo dari bisa dari a tare dasu.

A karshe tayi yiwa kannywood fatan cigaba tare da fatan ganin kannywood ta bukasa fiye da yadda take.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More