Shirya kama Ni da Gawuna yansanda suka yi – Sule Garo

Rundunar ‘yan sanda ta yi korafin cewa Kwamishinan Kananan Hukumomin na Jahar Kano da kuma shugaban Karamar Hukumar Nasarawa sun je cibiyar tattara sakamakon zaben, inda aka hargitsa takardun sakamakon zaben.

Kwamishina Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jahar Kano Alhaji Murtala Sule Garo a ranar Alhamis ya kalubalanci yadda abubuwan da jami’an ‘yan sanda suka gabatar a
matsayin dalilan da suka kama shi tare da mataimakin Gwamna Dakta Nasiru Yusif Gawuna a lokacin zaben Gwamna da ya gabata na Jahar Kano.

Yace duk da cewa ‘Yan Sanda sun bayyana cewa tsare mataimakin Gwamna yana nufin kariya ne dan kaucewa harin wasu a cibiyar tattara sakamakon zaben.

Mutala Sule Garo ya bayyana wa manema labarai cewa, sunje cibiyar tattara sakamakon zaben ne domin ganin abubuwan da suke farawa kamar yadda suka samu rahoton yunkurin da Hukumar zaben tare da hadin bakin wakilan Jam’iyyar PDP na kokarin sauya sakamakon zaben da Jam’iyyar APC ta samu nasara.

Kwamishinan Kananan Hukumomin Jahar Kano wanda aka bayar dashi kan beli ya zargi Wakilan Jam’iyyar PDP wanda suka batar da kama da suffar jami’an sa ido kan harkokin zabe inda suka kwace takardun sakamakon zaben tare da wasu muhimman takardu wanda kuma suka kala min da mataimakin Gwamnan Kano lokacin da muka isa cibiyar tattara sakamakon zaben.

Murtala Sule Garo ya yi watsi da bayanan da ‘Yan Sanda suka yi na cewa sun bawa Mataimakin Gwamna kariya a lokacin da al’amarin ya faru.

Sabanin cewa ni da Mataimakin Gwamnan da Kuma shugaban Karamar Hukumar Nasarawa sun kama mu kuma sun tsare mu har tsawon awanni a shekwatar hukumar ‘yan Sadan dake Bompai, Jahar Kano.

A karshe Sulen Garo yace zasu dauki dukkan matakan da ya dace na shari’a kan jami’an ‘yan sandan, tare da cewa yana da tabbaci na sake lashe zaben ga Jam’iyyar APC idan aka sake gudanar da zaben da aka tsara ranar 23 ga watan Maris 2019 idan akayi la’akari da gagaruman nasororin da gwmanatin ta samar zuwa yanzu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More