
Shugaba Buhari bazai yi murabus ba- Lai Muhammad
Me zaku ce gama wannan batun?
Gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai yi murabus saboda rashin tsaro ba, tare da bayyana cewa ba za ta ja baya ba daga shirinta na daidaita soshiyal mediya ba.
Kamar yadda na fada a baya, kasar na fuskantar matsalolin tsaro sannan ana magance matsalolin, sai dai akwai wasu kiraye-kiraye a kwanakin da suka wuce, wanda ke neman Shugaba Buhari ya yi murabus, ko ya tsige shugabannin tsaro. Ina so na sanar da cewar, gwamnati wacce ke ci gaba da samar da kayayyaki ga sojoji da hukumomin tsaro ta yarda da kokarinsu wajen magance rashin tsaro, kuma za’a magance wadannan matsaloli cikin nasara. Cewar Ministan Labarai da al’adu na kasa Lai Mohammed.
Ya kuma kara da shawarci dukkanin masu sharhi musamman shugabannin siyasa da na addini da su yi taka-tsantsan a wannan lokaci da ake ciki, ga kuma wayanda ke kira ga Shugaban kasa da ya yi murabus, ina fatan sanar da cewa, Shugaban kasa ba zai yi murabus ba domin yana da goyon bayan yan Najeriya na jagorantar su zuwa lokacin da wa’adin mulkinsa zai kare a watan Mayun 2023.