Shugaba Buhari ya kaddamar da sabbin jiragen yaki

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabin jiragen yaki guda 3 masu saukar angulu, mallakin rundunar Sojojin sama a kokarin da gwamnatinsa ta ke yi wajen ganin an shawo kan matsalar tsaro da suka addabi yan kasa Najeriya.

A yau Alhamis 6 ga watan Fabrairu ne shugaba Buhari ya kaddamar da jiragen a filin Eagle Square dake babban birnin tarayyar Abuja, guda biyu kirar Agusta 109P helicopter dayan kuma samfurin Mi0171E helicopter.

shugaba Buhari ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya karkashin shugabancin nasa za ta yi iya bakin kokarin ta don ganin ta magance matsalar tsaron da suka addabi yan Najeriya, inda ya kara da cewa, ba za ta baiwa yan Najeriya kunya ba.

Ya kuma nanata manufar gwamnatinsa na karkatar da alakar tattalin arzikin Najeriya daga man fetir domin samun karin kudaden shiga don gudanar da aikace aikacen daya sanya a gaba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More