Shugaba Buhari ya kafa kwamitin sulhunta rikicin APC da Majalisar Dokoki da Zartarwa

Macece shawarar da suka iya badawa game da wannan kwamitin da shugaba Buhari ya kafa?

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani kwamitin tuntubar juna tsakanin yan majalisar dokoki da bangaren zartarwa da kuma jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

Shugaba Muhammadu  Buhari ya kaddamar da kwamitin tuntubar, karkashin jagorancin mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, yayin da shugaban riko na jam’iyyar APC, kuma gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni, da shugabannin majalisar dattawa da wakilai yan jam’iyyar APC, da sakataren gwamnatin Najeriyar suka kasance yan kwamitin.

An kafa kwamitin ne da nufin magance rikicin da ake samu a tsakanin bangarorin, tare da inganta harkar mulki da rayuwar al’ummar kasar ta Najeriya.

Sai dai wasu masana na ganin cewa an so a makara wajen kafa kwamitin.

Shugaba Buhari bai fito ya fadi nau’o’in rigingimun da suka addabi jam’iyyar APC mai mulki da kuma irin takun-sakar da ake samu tsakanin bangaren zartarwa da yan majalisar dokokin Najeriyar ba, wanda suka wajabta kafa kwamitin.

Sai dai  ya ce bangaren zartarwa ba shi da niyyar amfani da kwamitin wajen tankwara yan majalisa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More