Shugaba Buhari ya karbi maganin gargajiya na Madagascar

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi maganin gargajiya na Madagascar da Shugaba Rajoelina ya ce yana maganin annobar cutar Coronavirus .

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, mallam Garba Shehu ya fitar da sanarwar cewa Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo a yau Asabar 16 ga watan Mayu 2020, inda ya karfi maganin daga hannun sa tare da gabatar da maganin gargajiyar na Madagascar data rabawa kasashen Afrika.

Sai da sanarwar bata bayyana adadin yawan maganin da Najeriya ta karba daga shugaba Embalo na Guinea Bissau ba.

Bayan karbar samfurin maganin ne,shugaba Buhari ya ce ba za a fara amfani da shi ba har sai masana kimiyya sun tabbatar da ingancinsa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More