Shugaba Buhari ya lashe zabe da kuri’u 15,191,847

Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zaben Najeriya a karo na biyu, bayan da sakamakon da aka tattara ya nuna cewa ya yi wa abokin hamayyarsa gagarumar tazara.

Shugaban mai shekara 76 ya kayar da Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, da tazarar kuri’u kusan miliyan hudu.

Jam’iyyar adawa ta PDP, wacce Atiku ya yi wa takara, ta yi watsi da sakamakon zaben.

Tun a sakamakon farko-farko da aka fara bayyanawa jam’iyyar ta yi zargin cewa akwai kura-kurai a zaben.

An samu jinkiri da kuma tashin hankali gabanin da kuma lokacin zaben sai dai masu sa’ido masu zaman kansu ba su ce an yi magudi ba.

Shugaba Buhari ya yi nasara a jihohi 19 daga cikin 36 na kasar, yayin da babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar ya samu jihohi 17 da kuma babban birnin kasar Abuja.

Buhari na APC ya samu kuri’u 15,191,847, yayin da Atiku na PDP ya samu 11,262,978, kamar yadda Hukumar Zabe ta INEC ta bayyana.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More