Shugaba Buhari ya rantsar da Sabbin sakatarori  na dindindin guda hudu a yau

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar  da Sabbin sakatarori na dindindin guda huda a fadar sa dake babban birnin Abuja a yau Laraba 30 ga watan Satamba 2020.

An gudanar da takaitaccen bikin rantsuwar  ne kafin a fara taron majalisar zartawa ta tarrayya wato FEC  wanda aka saba gudanarwa a duk sati

An rantsar da  sakatarorin 12 a watan Yuni, inda sabbin 4 suka cika 16.

 Wanda aka rantsar a yau sun hada da mace da maza uku kamar haka:

Mista James Sule daga Jahar Kaduna
Ismaila Abubakar  daga jahar Kebbi
Misis Patricia Robert daga jahar River sai Mista Shehu Aliyu Shinkafi daga jahar Zamfara.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More