
Shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan 12 ga watan Yuni
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutun ma’aikata na kowace shekara tare da amincewa da ranar a matsayin ranar Dimokaradiyya.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar dattawa Sanata Ita Enang, ne ya bayyanawa sanarwar hakan a ranar Litinin 11 ga watan Yuni 2019.
Sanata Ita, ya ce an soke hutun ranar ma’aikata da aka saba yi a kowace ranar 29 ga watan Mayu a Najeriya inda aka maya shi da gurbin 12 ga watan Yuni.