Shugaba Buhari ya rattaba hannu aka dokar hana yin ba-haya a fili

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu akan wata doka da ta hana yin ba-haya ko fitsari a bainar jama’a da kuma wasu al’amuran da suka shafi hakan.
An yi wa dokar lakabi da “kawar da matsalar ba-haya a fili a Najeriya nan da shekarar 2025.”

Ministan ma’aikatar Ruwa na Najeriya, Inginiya Suleiman Adamu, ya bayyana cewar an yi dokar ne don tabbatar da an samar da tsafta muhalli da ruwan sha a kasar ta Najeriya.
Kasar Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke fuskantar matsalar ba-haya ko fitsari a fili, yayin da lamarin kan haifar da illoli ga lafiyar dan adam.
Indiya ita ce kasar da ta fi kowacce fuskantar wannan matsalar a duniya, amma ta dauki wasu matakai na kawo karshen hakan.

A yanzu hukumomin a Najeriya su ma sun dukufa wajen ganin an tsaftace ko ina.
Dokar dai ba tana nufin idan aka samu mutum da laifin yin ba-haya a bainar jama’a za’a hukunta shi ba ne, ana so jama’ su dauki dabi’ar tsaftace muhallansu da kansu ba tare da wani ya tsawata masu ba.

Ministan ya kara da cewar, an umurci ma’aikatun gwamnati da su samar da wadattattu da tsaftatattun makewayi a duk ofisoshinsu, sannan gwamnatocin jahohi da na kananan hukumomi ma su bi sahu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More