Shugaba Buhari ya rattaba hannu akan kasafin kudin 2020

Sauye-sauyen da majalisa tayi wa kasafin kudin Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan sabon kasafin kudin da Najeriya za ta yi amfani da shi a shekarar 2020 mai zuwa, a ranar Talata 17 ga watan Disamba 2019.

An samu sauye a tsakanin kasafin kudin da shugaban kasar ya gabatarwa majalisa a watannin baya, da kuma kundin kasafin da ya sa wa hannu bayan an yi wasu kwaskwarima.

  1. Adadin kudin da za a kashe

Shugaba Buhari ya sa ran kashe naira tiriliyan 10.33 ne a shekarar badi. Amma majalisar tarayya sun kara buri, inda su ka yi sama da kudin da za a batar da biliyan 260 zuwa naira tiriliyan 10.56.

  1. An kara yawan kudin albashi

Majalisar tarayya ta kuma kara yawan abin da gwamnatin Najeriya za ta batar a kan albashi a 2020. Buhari ya yi lissafin naira tiriliyan 4.84, sai majalisa ta kara miliyan 400 zuwa tiriliyan 4.84.

  1. Ayyukan more rayuwa

Kamfanin BudgIT mai bin diddikin yadda ake kashe kudi a Najeriya ta bayyana cewa kudin da aka ware domin ayyukan more rayuwa sun tashi daga tiriliyan 2.45 zuwa tiriliyan 2.72 a 2020.

  1. Kudi wasu hukumomi

Kudin da ake warewa wasu ma’aikatu masu cin gashin kansu kamar majalisa, bangaren shari’a, da irinsu INEC, ya karu. Abin da za su kashe yanzu ya tashi daga miliyan 556 zuwa miliyan 560.

  1. Biyan bashi

Haka zalika majalisar tarayya ta yi kwaskwarima game da batun kudin bashi. Abin da Najeriya ta ware domin biyan bashi a kasafin kudin badi ya koma naira tiriliyan 2.72 daga tiriliyan 2.45.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More