Shugaba Buhari ya roki yan Najeriya dasu kara hakuri bisa karancin makaman yaki

Menene shawarar da zaku iya badawa?

Shugaba kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya roki al’ummar kasar da su kara hakuri game da matsalolin tsaro da ake fuskanta, inda ya ce suna “bakin kokarinsu wurin sayo karin makamai” don karfafa ayyukan tsaro.

Shugaban ya bayyana haka ne ranar Litinin a wani sako da ya wallafa a shafukan zumunta, yana mai cewa tuni suka sayo wasu makaman, ana tantance wasu a gabar ruwa sannan kuma ana kera wasu.

“Muna matukar kokari wurin tabbatar da cewa mun bunkasa harkokin tsaro a wasu sassa na Najeriya kuma daga cikin kokarin muna kashe kudi masu yawa wurin sayen makamai,” in ji Buhari.

“Ina rokon a kara hakuri kan maganar sayen makamai musamman saboda tasirin annobar Coronavirus a kasashen da ke samar da su, idan kayan aikin sun iso, sai mun bai wa jami’an tsaro horo kafin fara amfani da su.”

A makon da ya gabata an kashe mutum aƙalla 30 a Kudancin Jahar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar a rikicin ƙabilanci da ‘yan fashin daji da ya ƙi ci ya ki cinyewa.

Kazalika jahohin Katsina mahaifar Buhari, Zamfara da Sokoto na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga masu amfani da babura tare da kashe daruruwan mutane.

Mazauna Katsina sun gudanar da wata zanga-zangar nuna ɓacin ransu game da yadda gwamnati ta gaza kare rayukansu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More