Shugaba Buhari ya sassauta dokar hana fita a jahohin Abuja, Legas da Ogun

Sassaucin zai fara daga karfe 9:00 na safiyar Asabar 2 ga watan Mayu. Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya a daren yau Litinin 27 ga watan Aprilu 2020.

Buhari ya ce: “Dokar ta hana fitan da ake kai a yanzu za ta ci gaba da aiki a Abuja, Legas da Ogun har sai wadannan sabbin matakan sun fara aiki ranar 2 ga watan Mayun 2020 da karfe 9 na safe.

“Duba da wannan da kuma shawarwarin kwamitin fadar shugaban kasa na musamman da ke yaki da Coronavirus da kungiyar gwamnoni, na bayar da umarnin sassauta matakan Hana fita a Abuja, Legas da Ogun daga ranar Asabar 2 ga watan Mayun 2020 daga karfe 9 na safe.

“Burinmu shi ne mu samar da tsari da zai tabbatar da cewa tattalin arzikinmu ya ci gaba da aiki a yayin da a hannu guda kuma za mu ci gaba da daukar tsauraran matakai kan yaki da annobar cutar ta Covid19”

Wadannan matakai irin su ne shugabannin kasashe suka dauka a fadin Duniya. “Sai dai bayan wannan sassauci za a sanya tsauraran matakai na tabbatar da yin gwaji da bin sawu, yayin da harkokin kasuwanci da na tattalin arziki kuma za su farfado. “Za a ba da damar shiga da fita da kayayyakin bukatu tsakanin jahohi”

Za mu tabbatar da cewa ana amfani da takunkumin rufe fuska a cikin taron jama’a tare da tabbatar da ana bin dokar bayar da tazara. “Amma dokokin hana taron addini da na shakatawa na nan za su ci gaba da aiki.

Ana son gwamnatocin jahohi da kungiyoyi su dinga samar da takunkumin rufe fuska ga ‘yan kasa.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More