Shugaba Buhari ya taya al’ummar musulmin Duniya murna zagayowar watan Ramadan

Shugaba kasar Najeriya Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce bai kamata Musulmi su dauki annobar Coronavirusa matsayin uzurin kin yin azumin watan Ramadana ba.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce yana taya dukkanin Musulmin duniya murnar shiga watan mai tsarki da falala

Sai dai Buhari ya gargadi masu azumin da su takaita al’adun cakuduwa da aka saba lokacin azumin watan Ramadana kamar yayin sahur ko kuma buda-baki.

Ya ce mutane su rinka cin abinci da gudanar da salloli a daidaiku ko kuma tare da iyalansu a gidajnsu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More