Shugaba Buhari ya taya Obasanjo murna cika shekaru 82 a duniya

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya taya tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo, murnar kara shekara daya a kan shekarun sa.

Mai bawa shugaban Najeriya shawara a fannin yada labarai, Malam Garba Shehu, ta bayyana cewa shugaba Buhari ya taya Obasanjo murnar cika shekara 82 a duron duniya.

“Duk da banbance-banbancen siyasa da muke da su da Obasanjo, ina ci gaba da kallonsa a matsayin mutum mai matukar kima, saboda irin gudunmuwar da ya bawa kasar Najeriya .

Buhari ya kara da cewa, “Cif Obasanjo, ya nuna halayen da za a yi koyi da shi sannan ya kwadaitar da na kasa da shi da irin dabarun iya shugabanci da yake da su.”

A cewar Buhari, mika mulki da Obasanjo ya yi ga gwamnatin farar hula a watan Oktoban shekarar 1979, na daga cikin irin gudunmuwar da ya bayar wajen ci gaban kasa Najeriya.

A karshe shugaba Buhari ya yiwa Obasanjo fatan Alkairi da kuma lafiya mai daurewa.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More