Shugaba Buhari ya umarci kwastam ta saki shinkafa don rabawa yan’Najeriya

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin raba wa ‘yan gudun hijira da al’ummar da suke bukatar agaji shinkafar da aka kwace daga masu fasa kwauri tun lokacin da aka rufe iyakokin kasar.

Ministar kudi ta Najeriya Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed ta shaida wa BBC cewa yawan shinkafar ta kai tirela 150 daga cikin wadda hukumar hana fasa kwauri ta kwace daga hannun wadanda suka shigar da ita kasar ba bisa ka’ida ba.

Ta ce za a raba shinkafar ne ga mabukata a wani mataki na rage wa al’umma radadin matakan da aka dauka na dakile cutar coronavirus.

Ministar kudin ta Najeriya ta ce hukumar kwastam za ta mika wa ma’aikatar agaji shinkafar inda su kuma za su jagoranci raba ta ga al’umma

Sai dai ta ce ba ta san tsarin da ma’aikatar agajin za ta bi ba wajen raba wa mabukata shinkafar ga jama’a ba. “Ma’aikatar agaji ce ke da nauyin raba abincin ga jama’a,” inji ta.

Ta kuma ce shinkafar da za a raba wa jama’a na da inganci sosai, bayan an tambaye ta ingancin shinkafar da aka dauki lokaci tana ajiye.

“Shinkafar ce aka tara kuma za a raba wa al’umma,” inji ministar kudin ta Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More