Shugaba Buhari ya yi alhinin mutuwar mataimakin shugaban NGE

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana alhininsa bisa mutuwar mataimakin shugaban kungiyar editocin Najeriya (NGE), Malam Umar Saidu Tudunwada.

Tudunwada, tsohon shugaban gidan radiyon Kano da ‘Freedom’, ya mutu ranar Lahadi, sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a kan hanyarsa ta koma wa Kano daga Abuja.

A wani jawabi da kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Lahadi a Abuja, Buhari ya bayyana marigayin a matsayin kwararren dan jarida da ya yi aiki bisa dokokin aikin jarida.

“Aikin jarida aiki ne na taimakon jama’a, saboda ‘yan jarida ne ke zama idanun jama’a ta fuskar sanar da su aiyukan da gwamnati ke yi. Ina mai alfahari da marigayi Tudunwada saboda ya yi aikinsa bisa tsari da ka’ida, tarihinsa na aiki ya tabbatar.

A karshe   shugaba Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga kungiyar editocin Najeriya, gwamnatin jahar Kano da kuma iyalinsa, tare da basu hakurin jure rashinsa, kuma yayi wa mareigayin fatan shiga gidan aljanna.

Tudunwada ya rasu ne bayan wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da shi a hanyarsa ta komawa Kano daga Abuja tare da daya daga cikin matansa da diyarsa.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More