Shugaba Buhari ya yiwa ministan da ya kamu da Coronavirus addua’i

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi wa Ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama addu’ar samun sauki, bayan ya kamu da Coronavirus.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar, shugaban ya bayyana Mista Geoffrey a matsayin wani babban ginshiki a mulkinsa, kuma ya yaba masa kan irin kokarin da yake yi wurin dakile yaduwar cutar ta Covid19.

Mista Onyeama dai na daya daga cikin ‘yan kwamitin da shugaban kasar ya kafa domin yakar annobar cutar ta Coronavirus.

A ranar Lahadi 19 ga watan Yuli 2020 ne ministan ya ya fitar da sanarwar ya kamu da Coronavirus, a shafinsa na Twitter inda ya ce an tabbatar da ya kamu da cutar bayan an yi masa gwajin cutar karo na hudu.

A sakon da ya wallafa, ministan ya ce a yanzu haka ya kama hanyarsa ta zuwa wurin killace masu dauke da cutar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More