Shugaba Buhari yayi ganawar sirri da gwamnoni 3

Bayan ganawar  sirri da shugban kasa  Muhammadu Buhari yayi  tare da gwamnoni 3 daga yankin Kudu maso yammacin kasar ta Najeriya  a karkashin jam’iyyar APC  a fadar sa dake babban birnin tarayyar Abuja. Kamfanin dillancin labarai na NAN, ta ruwaito cewa, gwamnonin da suka yi ganawar sirrin da shugaban kasar sun hada da gwamna  jahar Ogun Ibikunle Amosun, Rotimi Akeredolu na jahar Ondo da kuma gwamna  jahar Ekiti Kayode Fayemi.

An ruwaito cewa, wannan taron da aka gudanar a sirrance, yana da nasaba   wurin   sasance  ‘yan jam’iyyar da suka samu matsala tun bayan zaben fidda da gwani da aka gudanar kwanakin baya da suka wuce.

Duba ba dacewa ba’a a san sakamakon zaman nasuba, amma hakan yana nuna cewar sasance a ke bukata da kuma dinke duk wata baraka dake tsakanin, dan fuskatar zabukan dake gabatowa  na 2019 a cikin kwaciyar hankali.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Comment moderation is enabled. Your comment may take some time to appear.