Shugaba Buhari yayi ganawar sirri da yarima Saudiyya

Shugaba kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da Yariman Saudiyya mai jiran gado wato Mohammed bin Salman, a Riyadh, dake babban birnin kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin Najeriya ta bada rahoton cewa da shugaba Buhari zai yi  ganawar kafin tafiya Makkah a yau ta babbar filin jirgin sama na  sarki Abdulaziz a Jeddah.

 Shugaba Buhari tare da tawagarda za su gabatar da Ibadar Umrah da Sallar Juma’a a masallacin harami dake Makkah.

 Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da sarkin masarautar Saudiyya, Sarki Salman, a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba, a Riyadh, inda suka tattauna yadda zasu hada kai musamman bangaren arzikin man fetur da iskar gas don samun cigaba.

Babban mataimakin shugaban kasa akan harka labarai Garba Shehu yace, shugaban Najeriya da na Saudiyya sunyi yarjejeniya kan yadda masarautar za ta sanya hannun jari a kamfanin man fetur da iskar gas na Najeriya da karfafa hadaka tsakanin Saudi Aramco da NNPC

 A ranar Litinin ne shugaba Muhammadu Buhari, ya bar Abuja zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin halartar wani taro na masu saka hannu jari (FII) da hukumar samar da kudaden kasuwanci ta kasar Saudiyyya (PIF) ta shirya.

An fara taron ne daga ranar 29 ga wata kuma za’a kammala ranar 31 ga watan Oktoba 2019.

 Tawagar ta shugaba Buhari ta hada  karamin ministan harkokin kasashen waje, Zubairu Dada, ministan kamfanoni, kasuwanci da saka hannu jari, Niyi Adebayo, karamin ministan man fetur Timipre Sylva, da ministan harkokin sadarwa  Dakta Ibrahim Pantami.

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More