Shugaba Buhari zai halarci taron zuba jari a birnin Landan

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafiya zuwa  birnin Landan a yau Juma’a 17 ga Janairu 2020 domin halartar taron zuba jari na Birtaniya da Afirka.

Wanna shine tafiyar farko da shugaba Buhari yayi a shekarar 2020, za’a gudanar da taron ranar

Litinin 20 ga watan da muke ciki, Firai Minsitan Birtaniya Boris Johnson mai saukar bakin.

Ana sa ran shugaba Buhari  zai hadu da shugabannin kasashen Afirka da manyan ‘yan kasuwa na duniya.

Ana fatan taron zai samar da sabbin damarmakin kasuwanci da zuba jari da samar da ayyuka, wanda zai amfani nahiyar Afirka da Birtaniya.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More