Shugaba Buhari zai hallarci taron a birnin New York Wacce shawara kuke da ita a gareshi?

Shugaba Muhammadu Buhari zaiyi balagoro zuwa kasar Amurka taron gangamin majalisar dinkin duniya a birnin New York.

Wannan ya biyo bayan tawagar da shugaba Buhari ya tura wakilcin Najeriya a bikin rantsar da sabon shugaban taron gangamin wanda ya kasace dan Najeriya, Farfesa Bande Tijjani.

Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar cewa,  Shugaba Buhari zai tafi New York,  wato kasar Amurka ranar Lahadi domin halartar taron gangamin majalisar dinkin duniya karo na 74 da aka fara ranar Talata 17 ga watan Satumba 2019.

Taron gangamin na shekarar 2019 ta ya kasance na musamman, duba da cewa  dan Najeriya ke shugabantan taron na gangamin.

A ranar 4 ga Yunin 2019 ne aka   zabi wakilin Najeriya zuwa majalisar dinkin duniya, Farfesa Tijjani Muhammad Bande,  a matsayin shugaban taron gangamin majalisar ta 74.

Wannan shine karo na biyu a tarihi Najeriya, yayin da da Najeriya  zai rike matsayin bayan Manjo Janar Joseph Nanven Garba a shekarar 1989.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More