Shugaba Buhari zai rantar da ministocin sa menene shawarar ku ga ministocin?

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai rantsar da majalisar ministocinsa, don fara aiki gadan-gadan a wa’adi na biyu na mulkinsa, bayan lashen zaben da ya gabata na watan Fabrairu na 2019.

Sabbin ministocin 43 da majalisar dattawa ta tantance sun hada da mutum 12 da aka yi wa’adin farko da su, da kuma mata guda bakwai.

Ministocin da aka shiga NextLevel da su, sune:

Babatunde Fashola – Tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje

Rotimi Amaechi – Tsohon Ministan Sufuri

Ogbonnaya Onu – Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha

Adamu Adamu – Tsohon Ministan Ilimi

Sanata Chris Ngige – Tsohon Ministan Kwadago

Hadi Sirika – Tsohon Karamin Ministan Sufurin Jiragen Sama

Zainab Ahmad – Tsohuwar Ministar Kudi

Lai Mohammed – Tsohon Ministan Watsa Labarai

Musa Bello – Tsohon Minsitan Abuja

Abubakar Malami – Tsohon Ministan Shari’a

Sulaiman Adamu – Tsohon ministan ruwa

Baba Shehuri – Borno

Sabbin ministocin sune:

Sharon Ikeazor daga Anambra

Gbemi Saraki daga Kwara

Zainab Ahmed daga Kaduna

Sadiya Farouq daga Zamfara.

Ambasada Maryam Katagum daga Bauchi

Ramatu Tijani daga Kogi

Pauline Tallen daga Filato

Sheikh Isa Ali Pantami – Gombe

Sanata Godswill Akpabio – Akwa Ibom

Alhaji Sabo Nanono – Kano

Rauf Aregbesola tsohon gwamnan – Osun

George Akume – tsohon gwamnan – Benue

Timipre Sylva – tsohon gwamnan – Bayelsa

Sanata Olorunnibe Mamora – Legas

Sunday Dare – Oyo

Festus Keyamo – Delta

Sanata Tayo Alasoadura – Ondo

Mustapha Buba Jedi Agba –

Olamilekan Adegbite – Ogun

Mohammed Dangyadi – Sokoto

Abubakar Aliyu – Yobe

Sale Mamman – Taraba

Muhammed Mamood – Kaduna

Uce Ogar – Abia

Emeka Nwajuiba – Imo

Akpa Udo

Clement Abam

Zubair Dada

Adeniyi Adebayo – Ekiti

Mohammed Abdullahi

Osagie Ehenere

Bashir Salihi Magashi – Kano

Ministocin su ne za su taimaka wa  shugaba Buhari wajen tsarawa da aiwatar da alkawurran zabe da ya yi wa ‘yan Najeriya, a matsayinta na kasa mafi girman tattalin arziki a Afirka.

Ana sa ran bayan bikin rantsar da ministocin a yau Laraba 21 ga wata Agusta 2019, shugaban kuma zai kaddamar da majalisar zartarwa ta hanyar jagorantar zaman farko da sabbin ministocin nasa.

Kusan wata uku kenan aka shafe ana tafiyar da gwamnati ba ministoci tun rantsar da  shugaba Buhari a ranar 29 ga Mayu.

Ko da yake, a wa’adin mulkinsa na farko, shugaban bai nada ministoci ba  har sai bayan kusan watanni shida da karbar ragamar mulkin kasar.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More