Shugaba Buhari zai taimaka wa Akinwumi Adesina don ya ci zabe

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugaban bankin ci gaban Afirka wato African Development Bank (AfDB), Akinwumi Adesina, wanda ya fada cikin rikici.

Babban mai bai wa Buhari shawara kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ya bayyana cewa Shugaba Buhari zai yi tsayuwar daka domin tallafa wa Adesina a takarar da yake yi na lashe zabe a karo na biyu.

Sanarwar da Bashir Ahmad, mai taimaka wa Shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter a yau Talata 2 ga watan Yuni, ta ce an yi ganawar ce a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja.

Sai dai bai yi cikakken bayani kan ganawar ba.

BBC ta rawaito cewa, masu lura da lamura na ganin ganawar tasu tana da nasaba da rikicin da Mr Adesina ya fada a ciki na zargin da aka yi masa kan nuna ɓangaranci a bankin.

Wasu masu kwarmata bayanai ne suka zargi Mr Adesina da nada ‘yan uwansa a kan wasu manyan mukamai da kuma bayar da kwangiloli ga ‘yan uwa da abokansa. Sai dai ya musanta zarge-zargen.

Hukumar gudanarwar bankin ta ce tana yin nazari da gaske kan zarge-zargen da aka yi masa.

Amurka ta yi watsi da wani bincike da aka yi a kansa game da zarge-zargen – sai dai bankin ya wanke Mr Adesina daga aikata su.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More