Shugaba Buhari zai yi balaguro zuwa kasar Nijar

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zai yi tafiya zuwa kasar Nijar yauLitinin domin halartar taron kungiyar Ecowas ta cigaban tattalin arzikin kasashen Afirika ta Yamma.

Fadar shugaban ce ta fitar da sanarwar hakkan a ranar Lahadi, inda ta bayyana cewa taron zai mayar da hankali ne kan tattalin arziki da annobar coronavirus da kuma tsaro.
Za’a gudanar da taron ne a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ranar Litinin.

Taron na kwana daya, shi ne irinsa na 57.

“Shugaba Buhari zai samu rakiyar ministoci da sauran jami’an gwamnati kuma zai dawo Abuja bayan kammala taron,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More