Shugaba Muhammadu Buhari ya dauki Sabbin alkawura 9 wa yan Najeriya

Shugaba Muhammaud Buhari ya zayyana wasu abubuwa guda tara da ya ce zai mayar da hankali cikin shekaru ukun da suka rage masa domin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adeshina ya wallafa a shafinsa na Facebook, Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar sabbin jakadun wasu kasashe zuwa Najeriya.

Shugaba Buhari ya shaida wa jakadun cewa “a kokarinmu na ganin mun inganta tsare-tsarenmu na cikin gida da waje da kuma samar da ci gaba a Najeriya mun fahimci dole ne mu aiwatar da wasu abubuwa guda tara da ya kamata mu samu fifiko a ‘yan shekarun da suka rage mana.”

Abubuwa tara da Buhari ya alkawarta sune:

*Gina tattalin arziki mai dorewa

*Bai wa jama’a dama da yaye
talauci

*Samar da ilimi mai nagarta

*Inganta sha’anin noma domin samar da abinci har ma a rinka fitar da shi waje

*Samar da ingantaccen sufuri

*Samar da wutar lantarki tsayayya

*Inganta sana’o’i da masana’antu

*Samar da ingantacciyar lafiya ga ‘yan kasa a farashi saukakake

*Fito da hanyoyin yaki da rashawa da cin hanci da kuma inganta harkar tsaro

Amma shugaba Buhari ya bayyana cewa, abubuwan guda tara da ya lissafa suna kunshe a cikin “Kundin habaka tattalin arziki da dawo da martabarsa na Najeriya” da gwamnatinsa ta fito da shi domin inganta rayuwar ‘yan kasar ta Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More