Shugaba Muhammadu Buhari zai aurar da diyar sa Hanan

Ana shirin bikin auren Hanan Buhari

Daya daya cikin ya’yan shugaba Muhammadu Buhari na kasar Najeriya, Hanan na shirin aurenta bikinta

Rahotunni sun nuna, Hanan Buhari ta kusa zaman amaryar  Mohammad Turad.

Mohammed Turad, mai bawa tsohon gwamnan jahar Legos shawara ta musamman da kuma ministan ayyuka mai ci a yanzu wato Babatunde Fashola.

Turad dane a wajen tsohon dan majalisar wakilai, Alhaji Mahmud Sani Sha’aban wanda ya wakilci  Zaria daga 2003 zuwa 2007, sannan ya taba takarar gwamna jahar Kaduna karkashin Inuwa jam’iyyar Action Congress of Nigeria wato ACN.

Ana sa ran daura auren Hanna Buhari tare da Turad Mohammed  a ranar Juma’a 4 ga watan satamba 2020.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More