Shugaba Trump ya kari yiwa kasar Iran barazana

96

Normal
0

false
false
false

EN-US
X-NONE
X-NONE

/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}

Shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa Iran barazanar kai mummunar hari a kan cibiyar al’adun Shi’a idan ta maida martani akan harin da ya kashe babban jami’in sojanta wato Qassem Soleiman, a makon da ya gabata.

“Su dai a ganin su an amince su kashe mutanen mu, su azabtar da mutanen mu su dasa bama bamai a gefen hanya su hallaka mutanen mu, amma a ce bai yiwuwa mu kai hari a kan cibiyar al’adun Shi’a? hakan ba zai yiwu ba,” inji Trump a hirarsa da manema labarai a cikin jirgin Air Force One a daren ranar  Lahadi 5 ga watan Janairu 2020.

Sai dai bai fadi ainihin abubuwan da zai auna ba. Amma masana doka sun ce kai harin bam a kan cibiyar al’adun shi’ar zai zama take dokokin kasa da kasa, haka zalika a sakonsa na Twitter a safiyar ranar Lahadi ya ce Amurka za ta maida martani kan harin Iran, da kai hari mai tsanani.

 VOA ta rawaito cewa shugaban kasar ya fadawa manema labarai cewa yana nazarin fitar da bayanan sirri da suka kai shi ga ba da umarnin kashe Soleimani.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More