Shugaban EFCC Bawa ya bada shaida a shari’ar zambar kudin tallafin mai biliyan N1.4

Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed
Bawa, ya bayyana a gaban Kotun Koli ta Ikeja a ranar Laraba don ya ba da shaida a shari’ar zambar biliyan N1.4.
Shari’ar zamba ta shafi wani kamfanin mai, Nadabo Energy, wanda Bawa ya bayar da shaida tun farko kafin a nada shi a matsayin shugaban EFCC.
Bawa, wanda shi ne shaida na biyar da ya gabatar da karar, ya fada wa Mai Shari’a C. A. Balogun na Babbar Kotun Jihar Legas da ke zaune a Ikeja cewa wanda ake tuhumar ya yi amfani da takardun jabu don cin gajiyar tsarin tallafin Gwamnatin Tarayya.
Bawa a watan Fabrairu ya bayyana wasu takardu biyu a matsayinnwasika ta Imel tsakaninsa da Ullrich Afini Awani na Kamfanin Global Commodities Africa da Takardar
Shaida.
A ranar Laraba, shugaban EFCC ya gabatar da shaida ta hannun lauyan kotun, Saidu Ateh, ya ci gaba da bayar da shaida ta hanyar yin nazarin sakonnin email na wanda ake kara.
Ya ce imel din ya fallasa gagarumar damfara a cikin takardun da.kamfanin ya gabatar wa Asusun Tallafin Man Fetur.
Bawa ya ce bincikensa ya nuna cewa wadanda ake tuhumar sun dauki kimanin litar mai miliyan 6 daga babban jirgin mai zuwa jirginsu na haya.
“Bugu da kari, imel din ya kuma sanar da mu cewa wani Mista Jide Akpan shi ne wakilin jirgin ruwan.
“Mun gayyaci Akpan da ake magana akansa kuma a yayin binciken mu tare da shi ya tabbatar da cewa wanda ake kara na farko ta hanyar wanda ake kara na biyu ya jinkirta jirgin ne ya biya shi,” ya fadawa kotun.
An gurfanar da Abubakar Peters (Manajan Darakta), tare da kamfanin sa, Nadabo Energy Limited, a ranar 10 ga Disamba, 2012, a gaban Mai Shari’a L. Balogun na Babbar Kotun Jihar Legas da ke zaune a Ikeja, Legas kan laifukan da suka shafi neman kudi ta hanyar yin karya da kuma yin jabun takardu wanda ya kai biliyan N1, 464, 961, 978. 24.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More