
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince a bude makarantu don a rubuta jarabawa
Rahotunni sun na cewa, Shugaban kwamitin yaki da Coronavirus ta fadar shugaban kasa kuma Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa,za a bude makarantu ga daliban da ke shirin rubuta jarrabawa – ‘yan aji shida a firamare, da ‘yan aji uku na karamar sakandare da kuma ‘yan aji uku na babbar sakandare.