Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir yana gidan yari

An kai tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir gidan yarin Kobar mai cike da tsaro, kwanaki kadan bayan da sojoji suka hambarar da shi a mulki.
Rahotanni sun ce kafin wannan lokacin dai an tsare shugaban ne bisa daurin talala a fadar shugaban kasa.
An ruwaito cewa an tsare shi karkashin sa idon jami’an tsaro.
 
Watannin da aka shafe ana zanga-zanga a Sudan ya jawo aka hambarar da shugaban tare da tsare shi a ranar Alhamis.
 
Ministan harkokin cikin gida na Uganda Henry Oryem Okello, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa kasarsa za ta duba yiwuwar bai wa al-Bashir mafakar siyasa, duk da sammacin da kotun hukunta masu aikata miyagun laifuka ta uniya ICC ta aike masa.
 
Sai dai a matsayinta na mamba a ICC, dole ne Uganda ta mika Mista Bashir ga kotun idan har ya shiga kasar. Har yanzu dai ICC ba ta ce komai ba kan batun.
Kafin yanzu dai, ba a san inda Mista Bashir yake ba. Jagoran juyin mulkin Awad Ibn Auf, ya ce ana tsare da Mista Bashir ne a wani “amintaccen waje,”.
 
Sai dai shi ma daga baya ya sauka daga mukamin nasa.
Daga bisani sai aka nada Laftanal Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya, inda ya zama shugaban Sudan na uku cikin kwanki kadan.
 
Yanda BBC ta ta saka a shafin ta, masu zanga-zangar dai sun sha alwashin ci gaba da mamaye tituna har sai an samu sauyin mulki zuwa na farar hula.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More