Shugabannin APC sun hadu da Buhari bayan kayen jam’iyyar a Edo a sirrance.

Shugabannin APC sun hadu da Buhari bayan kayen jam’iyyar a Edo a sirrance.

Shugaban kwamitin rikon jam’iyyar All Progressive Congress (APC) na kasa, Mala Buni, da shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar karkashin jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje, sun gana da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin.

Kodayake an yi ganawar a bayan sirri kuma mahalarta taron ba su bayyana abubuwan da suka tattauna ba, ana jin jami’an jam’iyyar sun yi wa Shugaba Muhammadu Buhari bayani game da ayyukan jam’iyyar a zaben.

Gwamna Godwin Obaseki na PDP ya kayar da Osagie Ize-Iyamu na APC da wasu ‘yan takara 12 a zaben.

An ga Buni da Ganduje, gwamnonin Yobe da Kano bi da bi, suna barin ofishin shugaban kasa ta hanyar sirri, wai don kauce wa masu ba da rahoton Fadar Shugaban Kasa.

Shugaba Muhammadu Buhari bai je Edo ba don yakin neman zaben dan takarar jam’iyyarsa amma ya yi alkawarin tabbatar da ingantaccen zabe a jihar.

Wasu jami’an APC a Edo, sun zargi PDP da murde zaben. Amma, APC ba ta ce ko za ta kalubalanci sakamakon zaben a kotu ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More