Shugabannin ECOWAS za su sake tattaunawa kan rikicin Mali

Shugabannin kungiyar Yammacin Afirka Ecowa za su gudanar da taro na musamman ranar Litinin domin bayar da shawara kan matakan da za a dauka don kawo karshen rikicin Mali.

BBC ta rawaito cewa, taron wanda za su gudanar ta intanet na zuwa ne bayan ziyara sau biyu da manzonni da shugabannin suka kai Bamako, babban birnin kasar wadda ta gaza shawo kan rikicin da ke faruwa tsakanin Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta da ‘yan hamayya da ke son ya sauka daga mulki.

Shugaban Ecowas, wanda shi ne shugaban Jamhuriyar Nijar, Muhammadou Issoufou ranar juma’a ya bayyana cewa, zai dauki “tsauraran matakai” domin shawo kan rikicin kasar.

Gamayyar jam’iyyun adawa, wadda ake kira M5-RFP, ta yi watsi da kira-kirayen kafa gwamnatin hadin kan kasa – inda ta dage kan cewa dole Shugaba Keïta ya sauka daga mulki sannan a kafa gwamnatin rikon kwarya.

Yayin da su kuma, Shugabannin Ecowas suka dage cewa dole a bi kundin tsarin mulki wurin kawo sauyi a kasar ta Mali.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More