Sojoji sun ceto mutum 34 da aka yi garkuwa da su a Jahar Benue

Sojojin Najeriya sun ceto mutum 34 da aka yi garkuwa da su a Jahar Benue sannan suka kashe shugaban gungun masu garkuwar, kamar yadda da hedikwatar tsaron Najeriya ta fitar da sanarwar hakkan.

Sanarwar ta ce dakarun runduna ta musamman ta Operation Whil Stroke ne suka yi nasarar ceto su a wani hari da suka kai a karamar Hukumar Logo ranar Alhamis.

An sada dukkanin wadanda aka ceto din da iyalansu, a cewar sanarwar.

Hazalika BBC ta rawaito cewa sojojin sun kwato bindiga kirar AK-47 guda daya da kwanson harsashinta guda daya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More